エピソード

  • Shin Ya Kamata A Samar Da Dokokin Da Za Su Sa Ido Kan Amfani Da AI?
    2025/07/18

    Send us a text

    Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba.


    Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba.
    Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dacewar sanya doka gane da yadda mutane za su rinka amfani da fasahar AI.

    続きを読む 一部表示
    23 分
  • Dalilan Da Suka Sa 'Yan Najeriya Ba Sa Samun Adalci
    2025/07/17

    Send us a text

    Rashin samun adalci a Najeriya ba ya rasa nasaba da cin hanci da rashawa a bangaren shari’a, inda ake zargin wasu jami’ai suna karɓar kuɗi kafin su yanke hukunci, kamar yadda manazarta suka bayyana. Ko mece ce gaskiyar wannan lamari?


    Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

    続きを読む 一部表示
    20 分
  • Wa Zai Gaji Buhari A Fagen Siyasar Najeriya?
    2025/07/15

    Send us a text

    Gaskiya da rikon amana suna cikin dalilan da suka sa tsoon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi fice a siyasar Arewacin Najeriay.

    Wasu masana da ma makusantar tsohon Shugaban kasar dai suna ganin Arewa ta yi rashi kuma zai yi wuya a samu makwafansa.

    Yayin da ake binne marigayin, hankalin wasu 'yan Najeriya ya fara komawa ga yiwuwar samun wanda zai iya maye gurbinsa a fagen siyasar Najeriya.

    wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

    続きを読む 一部表示
    24 分
  • Abin Koyi Daga Rayuwar Marigayi Muhammadu Buhari-- Makusantansa
    2025/07/14

    Send us a text

    Rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa 'yan Najeriya da dama kaduwa duk da cewa ya jima yana fama da rashin lafiya.


    Sanar da rasuwar ke da wuya, 'yan kasa suka fara bayyana ra'ayoyi daban daban akan abin da suka gani game da rayuwar tsohon shugaban.

    Amma makusantansa sun bayyana wasu halaye game da shi wadanda ba kowa ne ya sani ba.


    Sune kuma shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

    続きを読む 一部表示
    25 分
  • Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki
    2025/07/11

    Send us a text

    Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba.


    Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya.

    続きを読む 一部表示
    25 分
  • Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
    2025/07/10

    Send us a text

    Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.


    Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Sarkakiyar Dake Gaban Hadakar ADC -- Atiku Ko Peter Obi?
    2025/07/08

    Send us a text

    'Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.


    Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane.

    Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027?


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari.

    続きを読む 一部表示
    27 分
  • Mene Ne Tasirin Nadin Mataimaka Na Musamman A Rayuwar Jama’a?
    2025/07/07

    Send us a text

    Wadanda aka zaba su rike mukaman gwamnati kan nada wasu mukarrabai don su taya su sauke nauyin da aka dora musu.


    Wasu na zargin nadin baya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga wadanda aka nada saboda rawar da suka taka yayin yakin neman zabe.

    Ko irin wadannan nade-nade na da wani tasiri ga rayuwar alumma?


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naden masu taimakawa shugabanni da irin tasirin da suke dashi.

    続きを読む 一部表示
    26 分